1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren harkokin wajen Amirka ya soki wasu kasashe

Zulaiha Abubakar
November 8, 2019

Sakataren harkokin wajen Amirka C ya soki kasashen Chaina da Rasha, yayin da ya ke shirin ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a ziyarar kwanaki biyun da ya ke gudanarwa a Jamus.

https://p.dw.com/p/3Shcu
Deutschland | US-Außenminister Mike Pompeo
Hoto: AFP/Getty Images/H. Hanschke

A lokacin da ya ke jawabi a gidauniyar Koerber gaban ministar tsaron Jamus Kramp-Karrenbauer, sakatare Pompeo ya bayyana yadda China ta ke cin zarafin 'yan fafutuka a yankin Xianjiang da Hong Kong, bayan ya zargi gwamnatin Chaina da bude shafin mulkin dannniya yanzu haka. Huldar jakadanci tsakanin Jamus da Amirka ta yi rauni karkashin mulkin shugaba Donald Trump wanda ke cigaba da sukar Jamus game da rawar da take takawa a batun shimfida bututun iskar gas daga Rasha.

A jiya Alhamis dai sakataren harkokin wajen Amirkan ya gana da takwaransa na Jamus Heiko Maas, nan gaba kadan kuma zai gana da shugabar gwamnatin Jamus da ministan Kudi Olaf Scholz, kafin ya kammala ziyarar gabanin bikin rushewar katangar Berlin din wanda zai gudana a gobe Asabar.