1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Michelle Bachelet na ziyara a kasar China

Binta Aliyu Zurmi
May 23, 2022

Shugabar hukumar kare hakkin bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta fara ziyarar aiki ta kwanaki 6 a kasar China, ziyarar da ke zama irinta ta farko a tsawon shekaru.

https://p.dw.com/p/4Bl33
Schweiz Genf | UN-Hochkommissarin für Menschenrechte Michelle Bachelet zum Ukraine Krieg
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Ziyarar da ta fara a yau Litinin za ta je har yankin Xinjiang, inda za ta tattauna da mutanen yankin domin duba zarge-zargen da ake yi wa mahukuntan kasar na cin zarafin mutane musamman 'yan kabilar Wiga da ake zargin sama da mutane miliyan guda ne ake tsare da su a wani sansani.

Tun a shekarar 2018 hukumar ta bukaci izinin kai ziyara yankin na Xinjiang, wanda sai a wannan karan mahukuntan na Sin suka amince.

Gabannin fara wannan ziyara Amirka da ke zaman doya da manja da China ta nuna damuwarta a kan abin da ta ce shugabar hukumar da wuya ta yi nasarar a binciken da za ta gudanar a kasar, kasancewar mahukuntan na Beijing sun sha musanta zargin cin zarafin al'ummar kasarta..