1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsinci gawar 'yar jarida a Mexiko

Ramatu Garba Baba
February 23, 2022

An tsinci gawar wata 'yar jarida da aka jima ana nema bayan da ta yi batan dabo a makon jiya. Ana zargin gungun masu fataucin miyagun kwayoyi da hannu a kisan.

https://p.dw.com/p/47SeM
Mexiko Protest gegen Morde an Journalisten
Hoto: Daniel Ricardez/EPA-EFE

Rahotanni daga Mexiko sun ce an gano gawar 'yar jaridar kasar mai suna Michelle Perez Tadeo, da aka shafe kwanaki ana nemanta ruwa a jallo. Masu aikin kashe gobara ne suka gano gawar da aka lullube aka kuma jefar a gefen wata babbar hanya a babban birnin kasar.

Ba a dai kai ga sanin musababbin mutuwarta ba tukun nan, amma 'yan sanda sun kaddamar da bincike. Yan jarida biyar aka kashe a Mexiko a cikin wannan sabuwar shekarar.

Masu rajin kare 'yancin aikin jarida sun nemi gwamnatin Mexikon, da ta gaggauta daukar matakin shawo kan matsalolin masu fataucin miyagun kwayoyi da manyan jami'an gwamnati da ake zargi da hannu dumu-dumu a cin hanci da rashawa, da ke kawo tarnaki ga aikin jarida, inda ake zarginsu da farauta dama hallaka 'yan jaridan da ke fallasa aiyukansu.