1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Özil ya mayar da martani kan hoto da Erdogan

Yusuf Bala Nayaya
July 22, 2018

Hoton da dan wasan na Jamus Mesut Özil ya dauka da Shugaban kasar ta Turkiyya ya sa ana masa kallo me fiska biyu musamman a tsakanin 'yan siyasa.

https://p.dw.com/p/31spR
FIFA Fußball-WM 2018 in Russland | Mesut Özil, Deutschland
Hoto: picture-alliance/GES/Thomas Eisenhuth

Dan wasan tsakiya na Jamus mai tushe da Turkiyya Mesut Özil ya bayyana cewa ba shi da wata manufa ta siyasa a dangane da hoton da ya dauka tare da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya kafin wasan kwallon duniya. A cewarsa tun yana karami mahaifiyarsa ta koya masa girmama manya da alfahari da kasar da iyayensa suka fito, don haka abu ne me wahala ya yi watsi da hakan.

Özil dan shekaru 29 da takwaran kwallonsa wanda shi ma ke da nasaba da Turkiyya Ilkay Guendogan sun tsaya sun yi hoto tare da Erdogan kafin wasan kwallon na duniya abin da ya haifar da cece-kuce na siyasa a Jamus.