1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Messi zai koma Inter Miami na Amirka

Mouhamadou Awal Balarabe
June 8, 2023

Lionel Messi na Ajentina ya yanke shawarar komawa Inter Miami na kasar Amirka da kwallon kafa maimakon Barcelona, inda zai samu kwatankwacin Euro miliyan 200 a kakar wasanni hudu.

https://p.dw.com/p/4SKMM
Lionel Messi ya taimaka wa Ajentina wajen lashe kofin duniya na 2022Hoto: Tom Weller/picture alliance/dpa

Fitaccen dan wasan kwallon kafa Lionel Messi zai fara taka leda a kungiyar Inter Miami da ke Florida na kasar Amirka. Zakaran kwallon duniya dan asalin Ajentina ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da jaridun da ke kula da lamuran wasanni na kasar Spain, bayan da ya yanke shawarar cewa ba zai koma FC Barcelona ba.

Shi dai Lionel Messi mai shekaru 35 da haihuwa ya buga wasansa na karshe a Paris St. Germain a karshen makon da ya gabata. Sai dai a baya-bayan nan, an yi ta cece-ku-ce kan wani yunkuri zuwa kasar Saudiyya don buga kwallo da zummar samun makudan kudade. Amma a kungiyar Miami, Messi zai samun kwatankwacin Euro miliyan 200 a kakar wasanni hudu.