1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20 sun rattaba hannu kan daftarin kare muhalli

Abdoulaye Mamane Amadou
June 29, 2019

Kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki na G20 sun cimma daidaito kan wani daftarin kare muhalli a babban taron kolinsu na duniya da suka gudanar a birnin Osaka na kasar Japan.

https://p.dw.com/p/3LJnS
Japan Osaka | G20 Gipfel | Bundeskanzlerin Angela Merkel und Olaf Scholz
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ce ta bayyana haka a yau Assabar tana mai cewa yarjejeniyar kare muhalli ta zo daidai da irin wacce kasashen suka cimma a shekarar bara, bayan shafe tsawon lokaci a na ta kai ruwa rana kafin nuna amincewar wasu kasashen game da ita.

Merkel ta ce daukacin kasashe 19 ciki har da Fransa da Jamus da China duk sun lamunta da wannan daftarin da ke kara jaddada yarjejeniyar birnin Paris kan batun dumamar yanayi baya ga Amirka kawai wacce da har yanzu ta ke ci gaba da nuna turjiya akai.