1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta mayar wa Trump martani

July 11, 2018

Jamus ta mayar wa Amirka martani dangane da kalaman cewar Jamus na gudanar da harkokinta ne yadda kasar Rasha ke bukata.

https://p.dw.com/p/31HUp
Brüssel Nato-Gipfel - Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Mori

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta mayar wa shugaba Donald Trump martani dangane da kalaman da ya yi na cewar Jamus na gudanar da harkokinta ne yadda kasar Rasha ke bukata.

Yayin da take kan hanyarta ta zuwa taron kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels na kasar Beljiyam a ranar Laraba, Angela Merkel ta ce Mr Trump ya sani cewa Jamus na da ikon zartar da abin da take so ba tare da an tsoma mata baki ba.

A wannan Larabar ce dai shugaban na Amirka ya zargi Jamus da zama 'yar amshin Rasha saboda wani shiri na fada bututun samar da iskar Gas tsakanin Rasha da Jamus din.