1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kare matakin dokar kulle

October 29, 2020

Merkel ta kare matakin gwamnatinta na sanya dokar kulle domin dakile sake bullar cutar corona a wani jawabi da ta yiwa yan majalisar dokoki ta Bundestag. 

https://p.dw.com/p/3kcaT
Deutschland Merkel Regierungserklärung Coronavirus Bundestag
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kare matakin gwamnatinta na sanya kwarya kwayar dokar kulle domin dakile sake bullar cutar corona a wani jawabi da ta yiwa yan majalisar dokoki na Bundestag. 

"Tace na fahimci damuwar da ake da ita musamman a wuraren da aka sanya tarnaki game da kullen. A halin da ake ciki ba mu iya gano kashi 75 cikin dari na sabbin kamun ba, a saboda haka akwai bukatar hanzarta daukar matakai domin shawo kan lamarin."

Jawabin nata ya zo a daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar sabbin kamun cutar a kullum inda a rana guda aka sami mutane 16,700 da suka kamu da cutar.

A ganawar da ta yi a ranar laraba da gwamnonin jihohi 16 na Jamus, sun cimma matsayar sanya kwarya kwaryar matakan kulle na wata guda domin dakile yaduwar cutar ta corona a fadin kasar.