1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kai ziyarar ba zata Afghanistan

May 10, 2013

Shugabar gwamnatin Jamus ta kai ziyarar bazata zuwa arewacin Afghanistan, ƙasa da makonni biyu da rasuwar sojan Jamus guda bayan da 'yan tawaye suka afka musu.

https://p.dw.com/p/18Vvf
Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) und Bundesverteidigungsminister Thomas de Maiziere (CDU) besuchen am 10.05.2013 im Feldlager in Kundus Soldaten der Bundeswehr. Merkel besucht für einen Tag die deutschen Truppen in Afghanistan. Foto: Kay Nietfeld/dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai wata ziyarar ba zata zuwa arewacin Afghanistan domin ganin dakarunta. Wannan na zuwa ne ƙasa da makonni biyu bayan da 'yan tawaye suka hallaka sojan Jamus guda suka kuma jikkata wani, a karon farko bayan shekaru biyu. Shugabar tare da dakarun sun yi adduo'i dan tunawa da mamaci.

Jamus ita ce kaɗai ƙasar da ke ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO da ta yi alƙawarin tura sojojinta zuwa Afghanistan domin horas da dakarun ƙasar har zuwa shekarar 2015, bayan ƙungiyar haɗin gwuiwar ta kammala janye dakarunta daga ƙarshen shekara mai zuwa. Wata ƙila Amurka ta amince ta tura nata idan hukumomi a Afghanistan suka yi alƙawarin basu kariya ta yin amfani dokokinsu.

Merkel da ta sauka a birnin Mazar-e-sharif da safiyar wannan juma'ar ta kai ziyarar ce tare da ministan tsaron ƙasar Thomas de Maizere. Wannan hafsan sojin ƙasar ya ce Merkel ba ta mutunta gwamnatin Afghanistan ba kasancewar ko ɗaya bata shaida musu niyyarta ta wannan tafiyar ba. Dakarun Jamus ne a mataki na uku wajen yawa daga cikin ƙasashen da ke aiki a ƙasar, inda take da dakaru fiye da dubu huɗu a yankin arewacin Afghanistan.

Merkel da tawagarta sun tuna da dakarun Jamus da suka rasu

Lokacin da ta ziyarci sansanin sojin Jamusawan da ke Kunduz ta je wurin da aka keɓe dan tunawa da dakarun Jamus da suka rayukansu a filin daga inda ta ce mutuwar kowani soja guda babban abun takaici ne a gare mu

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) besucht am 10.05.2013 im Feldlager in Kundus Soldaten der Bundeswehr. Merkel besucht für einen Tag die deutschen Truppen in Afghanistan. Foto: Kay Nietfeld/dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

"A madadin ɗaukacin al'ummar Jamus, ina mai jaddada muku cewa muna cigaba da mutunta ayyukan da sojojinmu su ka yi a nan, saboda ba taimakawa wajen tabbatar da tsaro a Afghanistan kaɗai su ke yi ba, suna bada gudunmawa kuma mai mahimmanci wanda zai tallafawa tsaron mu duka baki ɗaya"

To sai dai majiyoyin Jamus sun tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Jamus cewa ko shugaban ƙasar Hamid Karzai, ba shi da masaniyar ziyarar ta Merkel sai da ana saura mintoci kaɗan kafin jirginta ya sauka, inda ofishin jakadancin Jamus a ƙasar ya bada hujjar cewa sun yi haka ne bisa dalilai na tsaro.

Duk da cewa Jamus ta yi alƙawarin tura dakarun da zasu horas da jami'an tsaron na Afghanistan, akwai wasu sharuɗɗa da su ka gindaya, inda su ka buƙaci ganin an sami ci-gaba, musamman wajen gudanar da zaɓuka masu adalci, a kuma tabbatar da girkuwar tsarin siyasa domin samun nasara kan 'yan tawaye ba ta wurin amfani da matakin soji ne kaɗai za'a samu ba.

Matakin horas da Jami'an tsaron Afghanistan

Merkel ta kuma ce matakin da suka ɗauka na horas da dakarun Afghanistan da kuma miƙawa 'yan ƙasa aƙallar jagorancin al'amuran tsaronsu, duk da cewa shugabar gwamnatin ta shaida cewa an sami gagarumin cigaba, ta ce a cigaba da la'akari da cewa akwai sauran haɗarurruka da ke tattare da janyewar da dakarun za su yi

Akwai babban ƙalubale na shirye-shiryen janyewar, musamman idan muka yi la'akari da cewa a yayin da ake gudanar da ayyukan dole ne a waje guda, mu kuma mu tabbatar da cewa an kare lafiyar dakarunmu.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) besucht am 10.05.2013 im Feldlager in Kundus Soldaten der Bundeswehr. Merkel besucht für einen Tag die deutschen Truppen in Afghanistan. Foto: Kay Nietfeld/dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun daga shekara ta 2002 zuwa yanzu, dakarun Jamus 35 suka rasu a Afghanistan. A yanzu haka kuma, ta yi alƙawarin tura dakaru 800 domin horas da jami'an tsaron ƙasar.

Mawallafiya Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal