1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta halarci addu'o'in Yahudawa

October 9, 2019

Bayan harin da wani dan bindiga ya kai kan Yahudawa a gabashin Jamus, Shugabar gwamnati Angela Merkel ta ziyarci wajen addu'o'in Yahudawan a tsakiyar birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/3R020
Berlin Kabinett beschließt Klimaschutzpaket
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta halarci wajen addu'o'i ne saboda girmama wadanda suka rasa rayukansu a lamarin da tun fari ta nuna matukar rashin jin dadinta a kai.

Tuni ma dai hukumomin tsaron Jamus suka tabbatar da cewa wanda ya kai harin wani matashi ne Bajamushe dan shekaru 27, wanda kuma ake zargin yana da tsananin ra'ayi na kyamar baki. 

Lamarin ya kuma kai ga shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin, nuna matukar bacin rai a kan wannan hari na kyamar Yahudawa.

Shi ma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi tir da faruwar lamarin.

Mutane biyu ne dai aka tabbatar mutuwarsu a harin na birnin Halle da ke gabashin Jamus, wanda ya zo a daidai lokacin da suke bikin ranar Yom Kippur da suke gudanarwa duk shekara, a ranar kuma da ke da matukar muhimmanci a gare su.