1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta ziyarci Sanchez

Abdul-raheem Hassan MNA
August 11, 2018

Wannan ziyarar na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da kasashen biyu suka amince da yarjejeniyar mayar da 'yan gudun hijira daga Jamus zuwa Spain, inda suka fara neman mafaka.

https://p.dw.com/p/330yd
Merkel trifft Spaniens Premier Pedro Sanchez
Hoto: Reuters/M. del Pozo

Batutuwan 'yan gudun hijira ne dai jigon ganawar da ta gudana tsakanin Angela Merkel da sabon Firaministan kasar Spain Pedro Sanchez.

Shugabannin biyu sun kuduri aniyar tallafawa kasashen Afirka da aka fi samun masu hijira musamman kasar Maroko, a wani mataki na takawa 'yan gudun hijiran birki har sai an tantancesu kamin shiga Turai.

Kasar Spain dai ta kasance ta farko cikin kasashen kungiyar Tarayyar Turai da ta cimma yarjejeniyar karbar 'yan gudun hijira daga Jamus.

Daura da batun masu neman mafaka, shugabannin za su kuma tattauna batutuwa da suka shafi tattalin arziki da batun tsaro da taron kungiyar tsaro ta NATO.