Merkel ta bukaci Rasha ta himmatu wajen warware rikicin Ukraine
June 25, 2014Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna bukatar ganin karin matakai daga Rasha don warware rikicin gabashin Ukraine cikin lumana. A lokacin wata mahawara a majalisar dokokin tarayyar Jamus a birnin Berlin a kan kasafin kudin Jamus, Merkel ta yaba wa shugaban Rasha Vladimir Putin bisa matakan farko da ya dauka kamar na kin amincewa da yin kutsen sojoji a Ukraine. A lokaci daya kuma Merkel ta bukaci ganin wani ci gaba don samun sukunin fara tattaunawa mai dorewa bisa manufar gano bakin zaren warware rikicin. Merkel ta kuma jaddada karfin tattalin arzikin Jamus da rawar da kasar ke takawa a matsayin kashin bayan kasashe masu amfani da takardun kudin Euro. Da ta juya ga batun samar da aikin yi a lokacin mahawarar Merkel cewa ta yi.
"Jamus tana da karfi kuma za ta ci gaba da zama a haka, musamman idan ci gaban da ake samu a kasuwar kwadago ya dore kamar yadda aka samu a cikin lokatun bayan nan."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahmane Hassane