1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta bukaci mataki kan sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
April 28, 2020

Wajibi ne kasashen duniya su kara azama wajen daukar matakan kare sauyin yanayi yayin da suke daukar matakan shawo kan koma bayan tattalin arziki saboda annobar corona inji shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

https://p.dw.com/p/3bWq3
Petersberger Klimadialog
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da kuma jami'ai daga kasashe talatin sun tattauna yadda annobar corona ke shafar manufofin kasashen duniya kan sauyin yanayi.

Taron kolin kan sauyin yanayi karo na goma sha daya da aka yiwa lakabi da Petersberg Climate Dialog a turance wanda aka gudanar ta hanyar bidiyo ya tattauna halin da kasashe ke ciki game da batun sauyin yanayin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kasarta a shirye ta ke ta bada goyon baya na rage hayakin masana'antu ga kasashen tarayyar turai daga kashi 40 cikin dari zuwa kashi 55 cikin dari.

A jawabinsa sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga dukkan kasashe su jaddada kudirinsu na rage fidda hayakin Carbon dioxide da ke gurbata muhalli. .

"Yace kada mu manta cewa kasashe 20 masu cigaban masana'antu na duniya baki dayansu su ke da alhakin kashi 80 cikin dari na hayakin masana'antu da ake fitarwa a duniya su ne kuma ke da kashi 85 cikin dari na arzikin duniya. Wajibi ne dukkaninsu su rage hayakin masana'antu nan da shekara ta 2050."