1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta alkawarta ba da taimako ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jamus

June 5, 2013

Yayin ziyarar da ta kai a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa shugabar gwamnati, Angela Merkel ta yi alkawarin ba da taimkon kudi ga wadanda bala'in ya shafa.

https://p.dw.com/p/18joZ
German Chancellor Angela Merkel (C) inspects a flooded street near the Elbe river in the east German town of Pirna June 4, 2013. Pictured at left is Saxony State Premier Stanislaw Tillich. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: POLITICS DISASTER ENVIRONMENT)
Hoto: Reuters

Merkel ta ce tuni gwamnatin Tarayyar ta Jamus ta kebe Euro miliyan dari domin ba da wannan taimakon gaggawa daidai wa daida ga yankunan Bavariya da Saxony da kuma Thueringen da bala'in ambaliyar ruwan ya shafa. Merkel ta kuma ba da tabbacin duba yiwuwar ba da karin taimako in har wadannan kudade suka kasa. Ko da yake sannu a hankali ana samun raguwar ambaliyar a kudancin kasar to amma har yanzu da wasu wurare da ke cikin mawuyacin hali. Shugaban kasar Jamus, Joachim Gauck ya mika godiyarsa ga 'yan kwana-kwana bisa aikin da suka yi babu gajiyawa domin taimaka ma wadanda bala'in ya shafa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal