1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar mata: Merkel ta ce a samar da daidaito

Abdul-raheem Hassan AH
March 9, 2020

A jawabinta na mako Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce maza na da rawar takawa a tabbatar da dai-daiton jinsi ba mata kadai ba, ta bayyana haka ne kuwa saboda bikin ranar mata ta duniya (08-03-20).

https://p.dw.com/p/3Z2YG
Deutschland Integrationsgipfel: Merkel beklagt Rassismus und Islamfeindlichkeit
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Angela Merkel ta fadi haka ne cikin jerin bidiyon da ta wallafawa a jawabinta na mako, amma ta yi wannan tsokaci ne na musamman saboda ranar mata ta duniya. Shugabar ta ce mata za su samu damar dai-daito ne kadai idan maza suka daura damar ayyukan gida, musamman wurin kula da yara da sauransu. Merkel ta ce tabbatar da dai-dato a Jamus na zaman babban batu a kasar, duk da cewar an samu cigaba na kaso 76 cikin 100 na mata da ke aiki a Jamus.