1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar Merkel da Putin

Ahmed Salisu
August 18, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce rikicin Siriya da Ukraine da kuma takun sakar Amirka da Iran na kan gaba a tattaunawarta da shugaban Rasha Vladmir Putin a ziyarar da ta kai kasar.

https://p.dw.com/p/33NAJ
Deutschland Treffen Angela Merkel Wladimir Putin auf Schloss Meseberg
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Baya ga wadannan batutuwa, Merkel ta ce za ta tabo batun kare hakkin dan Adam a kasar Rasha da kuma dangantaka da ke akwai tsakanin kasashen biyu wanda ke da karfin fada a ji a duniya. Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce a ganinta abubuwa masu sarkakiya na bukatar a hau kan teburin tattauna wajen warwaresu. Wannan ne ma ya sanya ta ce ta ga dacewar tattaunawa kan wadanan batutuwan da shugaban na Rasha a ziyarar da yanzu haka ta ke yi a kasar.