1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da Putin sun gana kan rikicin Ukraine

July 13, 2014

Shugabannin kasashen na Jamus da Rasha sun bukaci da a gaggauta komawa kan teburin sulhu domin kawo karshen rikicin kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/1Cc9j
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma Shugaba Vladimir Putin na Rasha sun amince kan cewa rikicin Ukraine na da matukar illah kuma sun bukaci da a mayar da hankali sosai kan batun sulhu. Kakakin shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ne ya sanar da hakan inda ya ce shugabannin biyu sun cimma wannan matsayar ne yayin 'yar takaitacciyar ganawar da suka yi a Brazil gabanin wasan karshe da za a fafata tsakanin Jamus din da Argentina. Da ma dai shugabannin biyu sun saba tattaunawa kan batun na Ukraine ta wayar tarho inda Merkel ta bukaci Putin da ya yi amfani da damar fada a jin da yake da ita a gabashin Ukraine domin kawo karshen rikicin da ake fama da shi a yankin tsakanin dakarun gwamnatin Kiev da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal