1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Ba ma goyon bayan hari a Siriya

Abdullahi Tanko Bala
April 13, 2018

Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ta nanata cewa Jamus ba za ta yi amfani da karfin soja ba, yayin da wasu manyan kasashe ke bayyana aniyar amfani da matakin sojan a kan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Siriya .

https://p.dw.com/p/2w1kS
Merkel empfängt dänischen Ministerpräsidenten Rasmussen
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

Kalaman Shugabar gwamnatin ta Jamusdin  Angela Merkel na zuwa ne bayan ganawar kyautata hulda da ta wakana tsakanin Jamus da kasar Denmark, inda shugaban Denmark din ya bayyana matsayin kasar kan amfani da gubar da ake zargin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Siriya ta yi.

Angela Merkel ta kuma soki kasar Rasha kan kokarin da ta ke yi na hana hukumar sa ido kan makamai masu guba ta duniya yin aikinta kan zargin Siriya da amfani da iska mai guba. Merkel ta ki amsa tambayoyi har sau biyu da aka yi mata dangane da sakonnin da shugaban Amirka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na twitter dangane da batun cewa zai iya kai hari a Siriyan.

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce ya zuwa yanzu babu daya daga cikin kasashen Amirka ko Faransa da suka nuna shirinsu na kai wa Siriya hari.

Heiko Maas in Brüssel
Ministan harkokin wajen Jamus Heiko MaasHoto: picture-alliance/AP Photo/V. Mayo

Sai dai a nashi bangaren sabon mai kula da dangantaka tsakanin Jamus da kasashen Turai da nahiyar Amirka Peter Beyer ya ce wannan sako na Mr. Trump na iya zame wa Jamus kayar kifi a wuya.

Wani mai sharhi kan al’amuran gabas ta tsakiya Guido Steinberg ya shaida wa tashar DW cewa akwai ta yi wu masana harkokin tsaron Amirka sun bayyana wa shugaba Trump irin hadarin da kasarsa za ta iya fuskanta, muddin ya yi garajen shiga rikicin da kasar Rasha ke ciki.

Su ma dai bangarorin adawa a siyasar Jamus ba su yarda da hanyar da shugaban Amirka ke barazanar kamawa ba, na afka wa Siriyan da yaki.