1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dauki alhakin harin Sri Lanka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
April 23, 2019

Mahukunta a kasar ta Sri Lanka na zargin wata kungiyar 'yan ta'adda da ba a santa sosai ba a kasar da hannu a hare-haren bam da suka hallaka fiye da mutane 320.

https://p.dw.com/p/3HIEY
Sri Lanka Negombo Zerstörte St. Sebastian Kirche nach Anschlag
Binicike kan harin Sri LankaHoto: Reuters/A. Perawongmetha

A yayin da mahukuntan a kasar Sri Lanka suka ayyana dokar ta-baci biyo bayan munanan hare-haren bam da ake alakantawa da wata kungiyar kishin addinin Islama suka yi sanadi na rayukan mutane fiye da 320 sannan akalla mutum 500 suka jikkata a lokacin bikin Easter, tambayar da ake yanzu ita ce me yasa mahukunta suka kasa aiki da gargadin da hukumomin leken asiri suka bayar cewa akwai yiwuwar kai hari a kasar ba? Tun makonni biyu da suka wuce shugabannin hukumar leken asirin kasar suka janyo hankalin shugaban kasar cewa wata sabuwar kungiya da ake kira "National Thowheed Jamaath" na shirye-shiryen kai hare-haren, har ma suka mika wa shugaban sunayen wadanda suke zargin, amma ba a dauki wani mataki ba.

Binciken harin Sri Lanka

Sri Lanka Terroranschlag Trauer Ostern
Mutane na ci gaba da binciken 'yan uwansuHoto: Reuters/A. Perawongmetha

Yanzu haka dai hukumom a kasar sun dukufa wajen binciken ko kungiyar da ke ikirarin jihadi da ta kai harin, tana samun tallafi daga ketare. Hukumomi a kasar sun kame mutane da dama da suke zargi da hannu a harin, sai dai tambayar da ake ita ce shin ya ba a iya kaucewa wannan hari ba? Wata majiya na cewa an yi kuskure wajen musayar bayanai tsakanin shugaban kasa Maithripala Sirisena da Firaminista Ranil Wickremesinghe da kuma ministan tsaro. A kuma halin da ake ciki karamin ministan tsaro,  Ruwan Wijewardene ya fada wa majalisar dokoki cewa binciken farko ya gano cewa an kai harin ne don daukar fansa na wani harin da aka kai kan masallatan juma'a a kasar New Zealand.

An kame wasu da ake zargi da hannu a harin

Wannan duka na zuwa ne a daidai lokacin da iyalai da dangin wadanda harin na ranar Lahadi ya ritsa da su ke ci gaba da dandazo a gaban babban asibitin birnin Colombo don neman sanin inda 'yan uwansu suke. A halin da ake ciki wata sanarwa da kungiyar IS ta bayar ta ce 'ya'yanta ne suka kai hare-haren kunar bakin waken a Sri Lanka. Kimanin mutane 40 ke hannun hukumomin kasar a daidai lokacin aka fara aiki da dokar ta-baci wadda ta ba wa 'yan sanda da sojoji karin iko na tsare da kuma binciken wadanda ake zargi ba tare da jiran umarni daga kotu ba.