1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin duniya na taro kan corona

Ramatu Garba Baba
December 3, 2020

A wannan Alhamis shugabanin kasashen duniya kimanin 100 ke soma zaman taron kwanaki biyu na Majalisar Dinkin Duniya domin lalubo dabarun kawar da annobar corona daga doron kasa.

https://p.dw.com/p/3m9o6
UN-Sondersession zum 75. Geburtstag
Hoto: Mike Segar/Reuters

Samar da allurar riga-kafi da zai kai ga kowa da yadda za a ceto rayuka tare da farfado da tattalin arzikin duniya daga ta'asar annobar corona za su kasance abubuwan da mahalarta taron za su tattauna a taron na kwanaki biyu. Jagoran taron Volkan Bozkir, ya ce, burinsu, shi ne yadda kasashen duniya za su amince da murya guda, domin ganin an cimma matsaya a shirin kawar da cutar ta Covid-19.

Shugabanin kasashen Jamus da Faransa da Firaministocin Britanniya da Japan da kuma Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa na daga cikin wadanda ake sa ran za su yi jawabi yau a zauren taron. Wannan dai na zuwa ne, bayan da hukumar da ke tabbatar da sahihancin magunguna ta amince da ingancin maganin da kamfanonin Pfizer da Biontech suka samar, Britaniyya ta kasance kasa ta farko da za ta soma aikin bayar da riga-kafin cutar da ta riga ta hallaka mutum sama da miliyan daya da rabi tun bayan bullarta kusan watanni 12 a yankin wuhan na kasar China. Mutum fiye da miliyan hamsin corona ta kama a sassan duniya kawo yanzu.