MDD ta yi Allah wadai da cin zarafin mata a Kwango
October 15, 2010Talla
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a yankin gabacin Afirka da ke kula da yaki da cin zarafin Mata Margot wallstrom
ta bayyana fargabanta dangane da yadda sojojin gwamnatin ke ci- gaba da aiwatar da fyade da kuma kisa akan mata galibi yara kanana a gabacin Kwango.
Margot wacce ke magana a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin duniya. Ta yi gargadin cewa a kwai bukatar daukar matakai na gaugawa ga al'uma yankin wanda daman suka fuskanci lamarin fyade daga sojojin kasar Ruwanda da na 'yan tawayyen Mai Mai a cikin watan yuli da ya gabata.
Mawallafi:Abdurahaman Hassane
Edita :Abdullahi Tanko Bala