1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta kai kayan agaji Nagorno-Karabakh

October 1, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta isa yankin Nagorno-Karabakh a daidai lokacin da kusan dukkanin al'ummar yankin suka tserewa rikici bayan da gwamnatin Baku ta kwace ikon yankin.

https://p.dw.com/p/4X1H6
'Yan gudun hijirar Nagorno-Karabakh da suka tsere zuwa Armeniya
'Yan gudun hijirar Nagorno-Karabakh da suka tsere zuwa ArmeniyaHoto: Vasily Krestyaninov/AP Photo/picture alliance

Kakakin shugaban kasar Azerbaijan ya ce, tawagar ta MDD da ta isa yankin ta kai kayayyakin agaji ne. Wannan dai na kasancewa karo na farko cikin kusan shekaru 30 da wata kungiya ta kasa da kasa ta samu damar shiga yankin.

Karin bayani: Jama'a na tserewa daga Nagorno Karabakh

'Yan awaren Armeniya da suka shafe gomman shekaru suna iko da yankin sun amince da aje makamansu da kuma rusa gwamnatinsu domin komawa Baku bayan mamayar da Azerbaijan ta kaddamar na kwana guda a makon da ya gabata.

Kasar Faransa dai ta yi kakkausar suka ga Azerbaijan kasancewar sai da akasarin al'ummar yankin kimanin dubu 120 suka tsere kafin ta bai wa MDD damar shiga yankin Nagorno-Karabakh.