1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

MDD ta damu da karuwar ta'addanci a Afirka

August 4, 2021

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce ayyukan masu ikirarin jihadi na ci gaba da zama gagarumar barazana ga zaman lafiya a duniya.

https://p.dw.com/p/3yVzH
Belgien Brüssel | Antonio Guterres
Hoto: John Thys/REUTERS

A wani sabon rahoto da ya fitar, Antonio Guterres, ya ce hakan na kara fitowa fili ne ta la'akari da yadda kungiyoyin ke yada rassa a wasu kasashen Afirka da nufin kafa daulolin da suka ayyana a baya a kasashe irin su Siriya da Iraki.

Mr. Guterres wanda ya mika rahotan nasa ga kwamitin sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya a jiya Talata, ya ce kungiyar IS da wasu na ta'addanci na amfani da da tsaikon da annobar corona ta kawo wajen yada manufofinsu musamman ta Intanet.

Kasashen dai da Majalisar Dinkin Duniyar ta ambato a matsayin wuraren da suke baza rassan a Afirka, su ne Mali da Burkina Faso da Chadi da Kamaru da Najeriya da Nijar sai kuma Muzambik da kuma kasar Tanzaniya.