1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD na son a kawo karshen rikicin Siriya

Ahmed Salisu
May 19, 2020

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Siriya Geir Pedersen ya bukaci Amirka da Rasha kan su taimaka wajen ganin an kawo karshen rikicin Siriya din da aka shafe shekaru tara ana yinsa.

https://p.dw.com/p/3cRdM
Das Leben in Aleppo nach der Eroberung der Stadt von Syrischen Truppen
Hoto: picture-alliance/dpa/X. Hua

Pedersen ya ce a 'yan shekarun da suka gabata an samu damarmaki masu yawa na daidaita tsakanin masu rikici a kasar ta hanyar amfani da siyasa wajen ganin zaman lafiya ya wanzu, sai dai ba a yi amfani da su ba wanda hakan ya kara rura wutar rikicin.

A wani jawabi da ya yi gaban Kwamitin Sulhu na MDD, manzon na musamman kan rikicin na Siriya ya ce baya ga Washington da Moscow, Turkiyya da Iran da ma 'yan tawayen da ke kokarin ganin bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad za su iya taka rawar gani wajen shawo kan rikicin.

To sai dai kafin kaiwa ga cimma wannan nasara, dole ne kasashen da za su hau taburin tattaunawa kan wannan batu su kasance sun amince da juna kana su yi aiki kafada da kafada wajen ganin an cimma matsaya guda ta kashe wutar rikicin wanda tuni ya lakume rayukan dubban mutane.