1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta umurci jama'a su fice daga Khan Yunis

January 25, 2024

Isra'ila ta umurci mutanen da ke samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijra da aka kai wa hari a garin Khan Yunis da ke Zirin Gaza da su fice daga yankin.

https://p.dw.com/p/4bgg1
Hoto: Jehad Alshrafi/Anadolu/picture alliance

Sanarwar hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa na Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da hakan ne daga bakin 'yan gudun hijirar da suka ce dakarun Isra'ila sun ba su wa'adin zuwa karfe 5 na yammacin ranar Juma'a da su bar yankin.

Da dama daga cikin 'yan gudun hijirar na kokawa kan rashin inda za su koma. Yayin da fada ke kara kazanta a garin na Khan Yunis da ke Zirin Gaza, ba a sanar wa hukumar bukatar fara kwashe jama'a ba a cewar rundunar sojin Isra'ila.

Rundunar na amfani da shafukan sada zumunta ne wajen wallafa umurnin fara kwashe jama'a bayan kawanyar da suka yi wa yankin da suka takaita amfani da internet.