1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Fararen hula da aka kashe a yake-yake sun karu a 2023

Abdullahi Tanko Bala
June 18, 2024

Yawan mata da aka kashe a rikice rikice a duniya ya rubanya yayin da yawan yara da suka rasa rayukansu ya rubanya sau uku a 2023 a cewar rahoton hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya

https://p.dw.com/p/4hDUj
Tagaiyarar al'umma a yakin Israila a Gaza
Tagaiyarar al'umma a yakin Israila a GazaHoto: Evad Baba/AFP

Yawan yara da aka kashe a rikice-rikice sun rubanya sau uku a cikin shekara guda haka ma adadin mata da suka rasa rayukansu a rikice-rikice a shekarar 2023 ya rubanya sau biyu fiye da shekarun da suka gabata yayin da baki daya fararen hula da aka kashe yawan su ya tasamma kashi 72 cikin dari a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce hare haren da bangarorin da ke fada da juna suke kaiwa ya kai matsayin da ba za a lamunta da shi ba.

Yace bangarorin ba sa martaba hakkin dan Adam suna aikata kashe kashe da jikkata jama'a fararen hula inda lamarin ya zama tamkar ruwan dare.

Shugaban hukumar kare hakkin dan din ta Majalisar Dinkin Duniya yace a 2023 ofishinsa ya tattara alkaluma da suka nuna karuwar hasarar rayukan fararen hula. Yana mai cewa lamarin ya yi muni matuka a yankin Gaza inda bangarorin da ke rikicin suka yi buris da hakkin dan Adam da kuma dokokin kasa da kasa.