1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu ana cin zarafin jama'a a Burundi

September 18, 2020

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedin cewa har yanzu ba a sami wani sauki ba na cin zarafi da keta haddin al'umma a Burundi inda suka ce sabuwar gwamnatin ta kasa tabuka komai.

https://p.dw.com/p/3iexy
Burundi Gitega | Beerdigung des ehemaligen Präsidenten Pierre Nkurunziza: Evariste Ndayishimiye hält Ansprache
Hoto: Getty Images/AFP/T. Nitanga

Sabon rahoton da kwamitin binciken ya fitar kan Burundi yace fatan da jama'a suka nuna a karshen mulkin shekaru 15 na marigayi tsohon shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya gushe yayin da aka cigaba da cin zarafin al'umma tun bayan da shugaba Evariste Ndayishimiye ya hau karagar mulki a watan Juni.

Shugaban kwamitin Doudou Diene yace basu ga wani sauyi ba kawo yanzu.

Burundi ta fada cikin rikici tun shekarar 2015 lokacin da Nkurunziza ya nemi yin tazarce karo na uku ya kuma lashe zaben da 'yan adawa da dama suka kaurace masa.