1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chamisa ya soke rantsuwar kama aiki

Mouhamadou Awal Balarabe
September 14, 2018

Annobar kwalara ta sa Jam'iyyar MDC dage bikin jeka na yi ka na rantsar da madugun adawa Nelson Chamisa a matsayin shugaban kasar Zimbabuwe duk da faduwa zabe da ya yi.

https://p.dw.com/p/34sDi
Nelson Chamisa
Hoto: DW/P. Musvanhiri

Babbar jam'iyyar adawa ta Zimbabuwe MDC ta dage bikin rantsar da Nelson Chamisa a matsayin shugaban kasa, saboda annobar kwalara da ake fama da ita a babban birnin kasar Harare. Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin jam'iyyar Jacob Mafume bai bayyana lokacin da za su gudanar da bikin da ya zo a daidai lokacin da MDC ke cika shekaru 19 da kafuwa ba. 

Dama dai hukumomi sun haramta duk wani taron jama'a a wannan mako a birnin Harare saboda guje wa yaduwar cutar amai da gudawa da ta halaka akalla mutane 25 cikin mako guda. Ko da ita ma jami'ar birnin Harare ta dage bikin yaye dalibai da ta shirya gudanarwa a wannan Jumma'a.

Ita dai kasar Zimbabuwe ta saba fuskantar ja'ibar cutar kwalara sakamakon rashin wadataccen ruwa mai tsafta, inda a shekara ta 2008, annobar kwalarar ta kashe akalla mutane 4,000.