1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mbeki da Obasanjo sun isa kasar Ivory Coast

December 4, 2005
https://p.dw.com/p/BvI2

Shugaban ATK Thabo Mbeki da takwaransa na Nijeriya Olusegun Obasanjo sun isa a kasar Ivory Coast a yau lahadi don gudanar da shawarwari da nufin zaban FM a wannan kasa ta yammacin Afirka dake fama da rikici. Shugaba Mbeki ya fadawa gidan radiyon ATK cewar batun na samar da FM yana da muhimanci kuma yana bukatar a dauki matakan gaggawa don warware shi. Mbeki da shugaba Obasanjo wanda shine shugaban kungiyar tarayyar Afirka dake yin sulhu a rikicin, sun isa Ivory Coast din ne daga wajen taron kolin Afirka da Faransa da ya gudana a birnin Bamako na kasar Mali. Duk da kokarin yin sulhu da kungiyar AU ta shafe sama da wata guda ta na yi har yanzu kungiyoyin siyasar kasar sun kasa cimma daidaito game da mutumin da za´a ba mukamin FM na wucin gadi kafin a gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan oktoban shekara mai zuwa.