1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan IS da Turkiyya ta kama zau koma Jamus

Abdoulaye Mamane Amadou
November 4, 2019

Hukumomin a kasar Turkiyya sun bukaci kasar Jamus da ta karbi 'yan asalin kasarta 20 mayakan kungiyar IS da dakarun Turkiyya suka kama a arewacin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/3SPoi
Symbolfoto Reisepass vor IS-Flagge
Hoto: picture-alliance/Eibner-Pressefoto/Wuest

A wata hira da jaridar Stuttgarter Nachrichten ta kasar Jamus, daraktan yada labaran shugaban Turkiyya ya bayyana cewa kasarsa na bukatar cikakkiyar hulda madaidaiciya da kawayenta wajen yaki da ta'addanci, a yayin da shi kuwa ministan harkokin cikin gidan Turkiyya Suleyman Soylu ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai dangane da batun yaki da ta'addanci, inda ya bayyana cewa Turkiyya ba wani hotel din mambobin kungiyar IS da suka fito daga kasashen waje ba. Kalaman dai na zuwa ne a yayin da dakarun Turkiyya da kawayenta suka kama 'yan kasar Jamus hudu dukkaninsu mayakan jihadi na kungiyar IS a arewacin Siriya farkon watan jiya, baya ga wasu 16 da tuni suke hannun jami'an n a kasar Turkiyya.