1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Mayakan IS 5 sun tsere daga gidan yari

Ramatu Garba Baba
October 11, 2019

An fada cikin fargaba bayan da wasu mayakan IS da ke tsare a wani gidan yari a yankin nan da ake musayar wuta a tsakanin dakarun kasar Turkiyya da 'yan tawayen Kurdawa suka tsere.

https://p.dw.com/p/3RAWY
Syrien Kampf gegen den IS - SDF Soldaten in Baghuz
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Dana

Mayakan IS da aka zarga da laifin hannu a ayyukan ta'addanci fiye da dubu goma dai ake tsare dasu a gidajen yari dabam-dabam a yankin da mayakan Kurdawan ke da karfin iko. Kasashen duniya sun ci gaba da baiyana damuwa kan halin da za a sami kai ciki a sanadiyar kubucewar da suka yi daga gidan yarin.

Amirka da janye sojojinta ya tayar da kurar rikici a Siriyan, ta bakin ministan tsaronta Mark Esper ta ce ta shawarci gwamnatin Turkiyya da ta dakatar da hare-haren, amma ga dukkan alamu babu alamar ta amince da hakan. Amirkan dai ta yi gargadin cewa in har gwamnatin Ankara ta yarda fursunonin IS suka yi nasarar tserewa daga inda aka killacesu, to ta shirya daukar nauyin matsalolin da za su haifar. Yanzu haka tana shirin sanyawa kasar takunkumi a sakamakon afkawa Siriya.