1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan IS dubbai na zaune a Siriya da Iraki

Yusuf Bala Nayaya
August 13, 2018

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Litinin ya nunar da cewa akwai kimanin mayakan kungiyar IS 20,000 zuwa 30,000 wadanda suka yi saura a kasashen Iraki da Siriya, baya ga sauran kasashe.

https://p.dw.com/p/336oy
Syrien IS Kämpfer bei Hama
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com

Rahoton na masu sanya idanu daga MDD ya kuma kara da cewa akwai kuma wasu mayakan na IS kamar 3,000 zuwa 4,000 da ke da sansani a Libiya, sannan akwai wasu manyan mayakan kuma da suka sauya sheka zuwa Afganistan.

Har ila yau rahoton ya kara da cewa mayakan na IS da ke a Siriya da Iraki mafi akasari mayakan sakai ne daga kasashen ketare. Rahoton ya kara da cewa wasu kudade na hadahadar mai a Arewa maso Gabashin Siriya na fadawa hannun mayakan. A yankin Sahel kuwa mayakan na a iyakar Mali da Nijar ne sai dai tasirinsu bai kai na Al-Ka'ida ba da ke da alaka da Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JMIN).