Mayaka sun kwace kauye a tsakiyar Mali
January 30, 2020Talla
Rayuwar mutanen da ke kauyen Soloko na cikin hatsari tun bayan da mayakan suka ayyana kwace iko da garin, mazauna garin sun koka da jinkirin samun agaji daga jami'an tsaro. Kauyen Soloko shi ne kauye na karshe a kan iyakar Mali da kasar Mauritaniya, kauyen na kusa da wani ungurminn daji da ke zama sansanin duk 'yan ta'adda da ke alaka da kungiyar al-Ka'ida wadan da ke kai hare-hare a kasashen Sahel musamman Burkina Faso da Nijar da Mali.