1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maxime Mokom ya gurfana a gaban ICC

Abdourahamane Hassane
March 22, 2022

Tsohon madugun  kungiyar yan tawaye ta anti balaka Maxime Mokom, a karon farko  ya gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifuk  ta kasa da kasa (ICC).

https://p.dw.com/p/48t1D
Zentralafrikanische Republik Koui Rebell mit Waffen
Hoto: Reuters/B. Ratner

Ana zarginsa da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil Adama a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarun 2013 zuwa 2014.Maxime Mokom, dan shekaru 43,ya jagorancin kungiyar ta antibalaka ta mayakan sa kai akasari Kiristoci masu tsatsauran ra'ayi da aka kafa a shekara ta 2013, a matsayin martani ga kwace birnin Bangui da kungiyar Séléka, ta Musulmi ta yi wadda ke adawa da tsohon shugaban kasar François Bozizé.