Mawuyacin hali a Siriya
February 9, 2012Babu wata alamar da ke nuna cewa jami'an tsaron Siriya zasu daina kai hari kan masu boren nuna ƙyamar gwamnatin Assad. Bisa rahotannin da mazauna birnin Homs suka bayar, motoci masu sulke da sojoji sun yi wa birnin ƙawanya tun daga yammacin juma'ar da ta gabata, kuma su kan shiga su yi harbin kan mai uwa da wabi sanan sun janye.
Bacin haka bayanai kaɗan kawai ake samu daga birnin na Homs. Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ƙaryata hare-haren da dakarun ke kaiwa, kuma sun rubuta cewa 'yan ta'adda ne su ka yi sanadin da birnin Homs ke zaman tamkar wanda ke fama da yaƙin basasa.
Haka nan kuma mazauna birnin sun ba da labarin cewa babu wutar lantarki da tsabtatacen ruwan sha da ma kayayyakin masarufi. Har yanzu ana cigaba da kai hare-hare da makamai masu linzami. Gidaje kaɗan suka rage a tsaye, har da asibitoci ma sun faɗi. Ana bukatar magunguna cikin gaggawa kuma likitoci ƙalilan suka rage, taimaka wa masu rauni shi kan shi na tattare da hatsari saboda masu harbin sari ka noƙe. Ga dai bayanin da wani mazaunin Homs ya yi a wani bidiyo:
"Wannan wani gidan ƙasa ne a Bab Amr. Inda wasu fararen hula suka tsere daga gwamnatinsu. Sun fasa gidajensu suka kuma kashe yaransu. Wannan ba irin harin da baƙo zai kai ba ne. Wannan hari ne na gwamnatin da ke neman hallaka mu. Yara ma sun mutu sakamakon irin waɗannan hare-haren. Wannan wace irin rayuwa ce, mu riƙa ɓoyewa saboda gwamnati guda"
Shugabar hukumar kula dahakkin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya Navi Pillay a jiya laraba ta bukaci duniya da ta taimaka wajen tallafa wa Siriya. Kujerar naƙin da ƙasashen Rasha da China suka ɗare ya sa abubuwa sun zo ma shugaba Bashar al-Assad a sauƙaƙe. Bayan da ya tattauna da shugaban kungiyar hadin kan Larabawa Nabil El-Araby, Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya na tunani sake fadada tawagar masu sanya ido domin aika su zuwa Siriya a karkashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda aka yi a watan Janairu kafin shirin ya ci tura.
" An karya alkawura da yawa har a kimanin sao'i 24 da suka wuce. na tabbata cewa wannan mummunan rikicin na Siriya ba zai kai ga mummunar illa ba kankij, rayuka nawa ne za'a rasa kafin a shawo kan wannan kufcewar da rkici ke ya shiga wani yanayi na yakin basasa."
Wani ɓangaren 'yan adawan Siriyan sun yi kira ga ƙasashen waje da su kare fararen hula. Amma 'yan adawa a Homs suna so su rungumi kaddara a hanunsu su kuma kwato 'yancin kansu su kare kansu.
Tuni dama ƙasashen yamma da na Larabawa suka rufe maganar shiga tsakani. Lokacin da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya kai ziyara kasar yabada shawarar shawo kan rikicin, wanda ba lallai ne ya yi tasiri ba. da sa'an nan kuma ya karfafawa shugaba Assad baya.
Mawallafi: Ulrich Leidholdt/Pinaɗo Abdu
Edita: Ahmad Tijani Lawal