1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Rasha kan rikicin Siriya

June 9, 2012

Rasha ta ce ba za ta yi adawa da saukar Assad daga mulki ba, idan har shawarar yin hakan daga al'ummar Siriyar ta fito

https://p.dw.com/p/15BMM
Russian Foreign Minister Sergei Lavrov talks to reporters after meeting Syria's President Bashar al-Assad in Damascus February 7, 2012, in this handout photograph released by Syria's national news agency SANA. Lavrov began talks with Assad on Tuesday by saying Moscow wants Arab peoples to live in peace and the Syrian leader is aware of his responsibility, Russian news agency RIA reported. REUTERS/SANA (SYRIA - Tags: POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei LavrovHoto: Reuters

Rasha ta ce ba zata yi adawa da saukar Assad daga kujerar shugabancin Siriya ba idan har wannan mataki ya kasance sakamakon tattaunawar da za'a gudanar tsakanin 'yan Siriyan kansu ba wai sakamakon matsin lamba daga kasashen waje ba.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne ya bayyana hakan a wannan asabar. A wata ganawa da yayi da manema labarai ya kara da cewa kasarsa ta yi imanin cewa bai dace kasashen ketare su gindaya sharuddan da 'yan kasa zasu yi amfani da shi wajen samun maslaha kan matsalolin da suka addabe su.

Jami'an sanya idon majalisar dinkin duniya sun kai ziyara wurin da aka kai hare-haren baya-bayan nan. A ƙauyen Al-kubayr inda masu fafutuka suke zargin dakarun gwamnati da hallaka mutane da dama ran laraba, jami'an sun ce jini har a bangon gidaje.

Dangane da yawan mutanen da abun ya shafa har yanzu ba'a iya bayar da wasu bayanai ba. Tuni dai gwamnatin ta yi watsi da wannan zargi ta kuma ɗora alhakin wannan ta'asa kan ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

Rahotanni daga birnin Deraa sun kuma nuna cewa an ƙaddamar da wani sabon rikici, inda 'yan adawa suka ce dakarun gwamnati sun bindige mutane 20 har lahira. Manzon ƙasa da ƙasa kan rikicin Kofi Anan ya yi kira ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya cigaba da takurawa gwamnatin Bashar Al-Assad har sai ta bada kai bori ya hau. To sai dai Rasha ta ce tana nan kan bakanta na ƙin amincewa da wani matakin da zai yi amfani da ƙarfin tuwo.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi