1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Rasha akan rikicin Siriya

June 9, 2011

Rasha ta ce za ta hau kujerar naƙi ga duk wani matakin da kwamitin sulhun MƊD zai ɗauka akan Siriya

https://p.dw.com/p/11Xkc
Shugaban Rasha Medvedev(sahun farko a dama) tare da wasu jami'an gwamnatin sa.Hoto: AP

Ƙasar Rasha ta sanar yin Allah Wadai game da duk wani ƙudirin da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya zai ɗauka akan hukumomin Siriya, abinda ke ƙara ƙarfafa matsayin ta na hawa kujerar naƙi ga ƙudirin da ƙasashen yammacin duniya ke goyon bayan sa na yin suka ga matakan da gwamnatin ƙasar ta Siriya ke ɗauka wajen ƙoƙarin daƙile masu zanga-zangar neman sauyi a ƙasar. Wani kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Rasha ya bayyana cewar yanayin da ƙasar Siriya ke ciki baya yin barazana ga sha'anin tsaro da zaman lafiya na ƙasashen duniya.

Dama dai ƙasashen Birtaniya da Faransa da kuma Portugal ne suka rarraba wani sabon ƙudirin dake yin Allah Wadai ga Siriya - a dai dai lokacin da Amirka da sauran ƙawayen ta ke ƙoƙarin yin matsin lamba akan gwamnatin shugaba Basha al-Assad na ƙasar da ta kawo ƙarshen ƙaddamar da hare-hare akan masu boren nuna adawa da gwamnatin.

A makonnin baya bayannan ne dai Rasha ta zargi ƙasashen yammacin duniyar da laifin wuce - gona da iri game da tanadin ƙudirin da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya cimma bisa la'akari da irin hare-haren jiragen sama da suke kaiwa a ƙasar da sunan kare fararen hula, kana ta yi gargaɗin cewar za ta yi nazari sosai akan duk wani ƙudirin da za'a ɗauka game da rigingimun dake faruwa a ƙasashen Larabawa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu