1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin NATO game da makaman nukiliya

October 22, 2010

Ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO za ta ci gaba da ajiye makamanta na nukiliya.

https://p.dw.com/p/PlPl
Angela Merkel da Anders Fogh RasmussenHoto: dapd

A cikin jawabin da ya yi wa manema labarai, bayan ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a birnin Berlin, shugaban ƙungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen ya ce sabuwar dabarar ƙungiyar za ta hada ne da amfani da makaman nukiliya. Ya faɗi haka ne ana saura wata guda ƙungiyar ta gudanar da taro a birnin Lisbon na ƙasar Portugal. Ya ce wajibi ne NATO ita kuma ta dawwamar da makaman da take ajiye da su a matsayin garkuwa ga duk wata barazana da za ta fuskanta. Ya ce kamata ya yi duk wani yunƙuri na rage yawan makamai ya haɗa da duniya baki ɗaya. Merkel a nata ɓanagre ta ba da goyon banyanta ga Rasmussen. A ma makon da ya gabata sai da ta ba da shawarar ci gaba da shirin ƙasashen Turai na girka garkuwa makamai masu linzami, a matsayin mataki na kwance ɗamarar nukiliya, da ya janyo ka ce-na ce tsakanin Faransa da sauran ƙasashen Turai.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu