1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin kotun ICC game da rikicin Libiya

May 16, 2011

Kotun duniya dake shari'ar manyan laifuka ta zargi manyan jami'an ƙasar Libiya da aikata laifukan yaƙi

https://p.dw.com/p/11HQ6
Luis Moreno Ocampo, mai shigar da ƙara a kotun hukunta manyan laifukan yaƙi (ICC).Hoto: dapd

Babban mai shigar da ƙara a kotun hukunta manyan laifukan yaƙi dake birnin The Hague ya gabatar wa alƙalan kotun hujjojin neman samun izinin cafke shugaban Libiya Muammar Gadhafi da kuma ɗansa Saif al-Islam bisa zarge-zargen da suka shafi aikata manyan laifukan yaƙi akan bani-adama. Baya ga shi shugaban na Libiya da kuma ɗansa, mai shigar da ƙarar ya kuma sanya sunan shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar Abdallah al-Sunusi cikin jerin mutanen da ya ke son ya bincika game da laifukan yaƙin. A cewar mai gabatar da ƙarar Luis Moreno-Ocampo ko da shike shaidun daya gabatar suna da ƙarfi sosai amma kuma yana buƙatar ƙari, kuma ya ce ya yi amannar cewar alƙalan kotun za su sahhale masa ɗaukar matakin yin binciken:

" Na yi imanin cewar za su yi hakan, kuma ina ganin idan ka ga hujjojin za ka fahimci cewar Gadhafi ya mulki Libiya tare da sanya tsoro a cikin zuƙatan jama'a, kuma a yanzu Libiyawa suna kawar da wannan tsoron."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mohammed Nasir Awal