Matsayin China da Rasha akan Siriya
June 5, 2012A rangadinsa na kwanaki uku wanda ke zama na farkon irinsa a yankin Asiya tun bayan sake komawarsa karagar mulki a karo na uku, Putin ya nanata matsayin dangantakar ƙasashen biyu wa Hu jintao. A yayin wannan ziyara tasa dai ana saran Putin zai gana da shugabannin Iran da Afganistan, a gefen taron yankin, wanda ke zuwa makonni kalilan bayan soke ziyararsa zuwa Amurka. Ƙarin matsin lamba akan Syria wadda ke samun makamai daga Moscow dai, shine zai mamaye taron. Matsayin Beijing da Moscow akan rikicin na siriya dai, na ci gaba da yin karan tsaye wa ƙasashen larabawa dana tarayyar Turai, dangane da ɗaukar matakan ladabtarwa. A ranar litinin ne dai shugaban tarayyar turai Herman Van Rompuy ya shaida wa Putin a Rasha cewar, ya zamanto wajibi Duniya ta cimma matsayi kan rikicin na Siriya. Shima a farkon ziyararsa a yankin Gulf, ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Guido Westerwelle ya jaddada muhimmancin bin siyasa wajen gano bakin zaren warware rikicin.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe