1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkakiya kan kafa gwamnatin Thailand

Suleiman Babayo USU
May 16, 2023

Pita Limjaroenrat da jam'iyyarsa da ke kan gaba a zaben Thailand suna ci gaba da samun sarkakiya kan kafa sabuwar gwamnati, inda shugaban jam'iyyar zai zama firaminista.

https://p.dw.com/p/4RRm0
Zaben Thailand | Pita Limjaroenrat
Pita Limjaroenrat wanda yake neman zama firaministan ThailandHoto: JACK TAYLOR/AFP/Getty Images

A kasar Thailand jam'iyya mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai da ta samu galibin 'yan majalisa da shugabanta Pita Limjaroenrat suna ci gaba da fuskantar sarkakiya wajen kafa gwamnati bayan babban zaben da ya gudana a karshen mako. Shi dai Pita Limjaroenrat yana fata kan zaman firamnistan kasar na gaba.

Jam'iyyar ta Move Forward wadda ta fito da batun sarauta kiri-kiri lokacin yakin neman zabe tana ci gaba da gamuwa da cikas ganin duk sauran jam'iyyun suna cikin wadanda suka dade ana damawa da su kan harkokin kasar. Kuma ana gani tilas sabuwar jam'iyyar da ta samu gagarumin goyon bayan jama'a ta sassauta matsayi kan batutuwa da dama kafin ta samu kawance kafa gwamnatin Thailand ta gabata, kasar da ta saba da rudanin siyasa da juye-juyen mulki na sojoji shekara da shekaru.