Matsalar yinwa a Somaliya
July 11, 2012Tashe-tashen hankula, da ƙarancin ruwan sama na barazanar sake jefa al'ummar Somaliya cikin yunwa, abunda ka iya mayar da hanun agogo baya ga yunƙurin baiwa ƙasar tallafin abincin da ƙasashen duniya suka yi bara, lokacin da ta yi fama da matsanancin fari.
Ƙungiyar kare haƙƙin ƙanana yara ta Save the Children ce ta bayyana wannan lamari a cikin wani rahoton da fitar a makon da ya gabata. Hukumar jinƙan ta ce da yawa daga cikin 'yan Somaliyan milliyan ɗaya da rabi da suka rasa matsugunnensu a rikice-rikicen baya bayan nan zasu yi fama da waɗannan illoli kasancewar da yawansu na dogaro ne da amfanin gona, wanda wadatuwarsa ne zai kai ga raguwar farashin kayayyakin abincin a kasuwanni. Marion Mckeone Jami'a ce a ƙungiyar ta Save the Children:
Ta ce: "Akwai abubuwa da dama da ke janyo wannan matsala, ƙaruwar ƙananan rigingimun da ake samu a ƙasar tasaknin ɓangarori daban-daban, na sanya mutane ƙauracewa daga matsugunnensu. Saboda haka mutane suna guduwa su bar gonakinsu, kuma wajen ceton rayuwarsu ba su iya kulawa da gonakinsu da dabbobinsu, haka nan kuma akwai ƙarancin ruwan sama wanda wajibi ne ya yi tasiri kan yawan amfanin gonan da za'a girba"
Marion Mckeone ta cigaba da bayyana cewa girbin bana ba zai yi kyau sakamakon rahsin ruwan saman, kuma abun da za'a samu ba zaui wadaci jama'a ba, bugu da ƙari kuma, da yawansu basu gama farfaɗowa daga illolin farin da ya addabi ƙasar bara ba, har yanzu basu mayar da jiki ba kuma ba zasu yi wuyan kama cututtuka ba, musamman ƙananan yara waɗanda ko yaya wahala take ba zasu iya jure mata ba.
Ta ce: "A daidai wannan lokaci muna buƙatar tallafin abinci mai gina jiki, akwai fiye da yara dubu 300 da ke fama da cututtukan da ke da nasaba da ƙarancin abinci mai gina jiki. Akwai sansanonin sama da 500 a Mogadishu na kulawa waɗannan mutane da ke ƙauracewa amma kuma sukan iso ne a gajiye, sun kwana da kwanaki babu ko ruwan sha, da yawan su kuma da ƙananan yara wasu ma har sun mutu a saboda haka ne ma muke da wani shiri na taimaka masu da wuraren kwanciya, abinci da tsaftataccen ruwan sha da magunguna"
Ƙungiyar agajin dai ta yi kira ga sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da su bada nasu gudunmawar, wajen ganin a sauya alƙiblar tallafin da ake baiwa a ƙasar wajen yaƙi da wannan annoba da ke neman zama ruwan dare a ƙasar, wato a maimakon kai agajin abinci da zarar mutanen sun ji yunwa, ya kamata a samar da shiri wanda zai ɗore na wani tsawon lokaci, ya kuma rage raɗaɗin illoli makamantan waɗanda ƙasar ke fuskanta yanzu. A daa dai masu gudun hijiran sun tsallaka zuwa ƙasashe maƙota amma a wannan karon madam Mckeone ta ce ƙetara iyakokin na da wahala
Ta ce: "Sansanin 'yan gudun hijira a Dadaab da ke Kenya ya dain akarɓar 'yan gudun hijira, kuma ma ƙetara iyakokin na da hatsari, abunda ke faruwa shine mutanen suna gudun hijira a ƙasarsu wasunsu ma a kan hanya suke gina matsugunne da itatuwa da tsummakarai da ma dai duk wani abun da zasu iya samu"
A ciki da wajen Mogadishu akwai 'yan gudun hijira a jibge, babu abun ci babu na sha kuma babu masaniyar inda zasu samu waɗannan abubuwa da suka wajaba a kansu dan tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullun.
Mawallafiya: Pinado Adama Abdu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi