1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar 'yan gudun hijira a Libiya

March 4, 2011

Tarayyar Turai ta koka game da matsalolin da 'yan gudun hijra daga Libiya ke fuskanta

https://p.dw.com/p/10TnC
Kristalina Georgieva, kwamishiniyar kula da 'yan gudun hijra na EUHoto: AP

Rahotannin dake fitowa daga Libiya na nuni da cewar yawan 'yan gudun hijirar dake zuwa ƙasashen Tunisia da Masar domin neman mafaka daga rikicin Libiya ya zarta mutane dubu 100. Hukumomin bayar da agaji da kuma gwamnatocin ƙasashen waje sun bayyana cewar an ɗan sami daidaiton lamura game da yanayin, amma sun nuna fargabar yiwuwar fin ƙarfin su idan har an ci gaba da gwabza faɗa a ƙasar ta Libiya.

Kwamishiniyar kula da harkokin bayar da agaji a tarayyar Turai Kristalina Georgieva ta ce suna fuskantar ƙarancin kayayyakin agajin da ake samarwa jama'a, kuma an shiga cikin wani mummunan yanayi. Hakanan ta ce ƙwararru daga Majalisar Ɗinkin Duniya basu sami sukunin kaiwa birnin Tripoli ba.

Akwai wasu jiragen sama na ƙasa da ƙasa dake aikin jigilar dubbannin 'yan gudun hijira daga wurin shaƙatawar nan na Djerba dake Tunisia. Wasu ƙasashen Turai da suka haɗa da Jamus da Spain da Italiya da kuma Faransa suna tura wasu ƙarin jiragen ruwa da kuma jiragen sama domin jigilar 'yan gudun hijirar. Shugaban Amirka Barak Obama, shima ya umarci wasu jiragen yaƙin ƙasar Amirka da su shiga a dama dasu cikin aikin jigilar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala