1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro ta janyo rusa gwamnatin Burkina Faso

Ramatu Garba Baba
December 9, 2021

Firaministan Burkina Faso Christophe Joseph Marie Dabire da gwamnatinsa sun yi murabus a sakamakon matsin lamba na al' ummar kasar kan matsalolin tsaro.

https://p.dw.com/p/441Qw
 Christophe Dabire
Hoto: Olympia de Maismont/AFP

Firaministan Christophe Joseph Marie Dabire da gwamnatinsa sun yi murabus ne a yammancin ranar Laraba a yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da abin da jama'a suka kira, gazawar gwamnati wajen yakar mayakan jihadi da suka janyo asarar rayuka tare da hana zaman lafiya a kasar da ke yankin Sahel. Wannan shi ne karon farko a nahiyar Afirka da shugaban gwamnatin da mambobin majalisar ke yin marabus saboda matsin lamba daga al'ummar kasar.

Dokokin kasar Burkina Faso, sun tanadi daukacin gwamnatin kasar da ta yi murabus a yanayi irin wannan da aka sami firaministan da ya zabi ajiye mukaminsa, inda gwamnatin za ta kasance ta wucin gadi, har sai an kafa wata sabuwa, kamar yadda babban sakataren gwamnatin kasar Stephane Wenceslas Sanou ya kara tabbatarwa. 


Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ya shiga hali na tsaka mai wuya a baya-bayan nan, inda ya ke ci gaba da shan suka a sakamakon yawaitar hare-haren mayakan da ake zargi na al-Qaeda ne, musanman harin farkon watan Nuwamban da ya gabata, da yayi sanadiyar rayukan jami'an soji kasar akalla 49 dana wasu fararen hula.