1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tangal-tangal ɗin Euro

September 28, 2011

A yau laraba ne shugaban hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya gabatar da jawabi ga majalisar Turai dake birnin Strassburg dangane da halin da ƙungiyar ke ciki.

https://p.dw.com/p/12ieS
Jose Manuel Dura BarrosoHoto: picture alliance/dpa

Tare da kakkausan harshe shugaban hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso yayi kiran gabatar da wani tsarin haraji bai ɗaya akan hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai yana mai ƙoƙarin kakkaɓe sunansa daga ɗariɗarin da ake zarginsa da shi. A fafutukar kuɓutar da ƙungiyar daga abin da ya kira:"hali mafi munin da ta taɓa fuskanta" Barroso ke fatan ganin an yi gagarumin hoɓɓasa bisa manufa:

"Wajibi ne mu ci gaba da yin hoɓɓasa. Akwai buƙatar sajewar dukkan yankunan dake amfani da takardun kuɗin Euro da juna. Wajibi ne mu kammala gamayyarmu ta takardun kuɗi tare da wata cikakkiyar ƙungiyar tattalin arziƙi."

EU-Kommissionpräsident Barroso beim EU-Gipfel am 23.6.2011
Shugaban hukumar zartaswar ƙungiyar tarayyar Turai lokacin jawabinsa ga majalisar TuraiHoto: dapd

Tare da tafawa da guɗar wakilan majalisar ta Turai, Barroso ya mayar da martani akan kalaman da suka fito daga bakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban ƙasar Faransa Nikolas Sarkozy. A cikin watan agustan da ya wuce ne jami'an siyasar guda biyu suka ba da shawarar kafa wata hukumar tattalin arziƙi tsakanin shuagabannin gwamnatocin yankunan dake amfani da takardun kuɗin Euro a ƙarƙashin shugabancin Van Rompuy, shugaban kwamitin ƙungiyar tarayyar Turai. Barosso yayi kakkausan suka akan abin da ya ce babban kuskure ne a mayar da tattaunawar a tsakanin gwamnatocin ƙasashen a wawware. Abu mafi alheri shi ne a ƙara ƙarfafa kafofin ƙungiyar, wato ma'ana hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai:

"Hukumar zartaswar ita ce hukumar tattalin arziƙin ƙungiyar tarayyar Turai kuma a saboda haka ba a buƙatar wasu sabbin cibiyoyi."

Sai dai kuma a baya ga kiraye-kirayensa da kakkausan harshe Barroso bai bata wata tsayayyar shawara a game da matakan da suka cancanta a ɗauka domin fita daga matsalolin da ake fuskanta a yanzu ba. Sai dai a karon farko ya fito fili yana mai bayyana goyan bayansa ga shawarar ƙirƙiro cinikin hannayen jari bai ɗaya tsakanin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai, wanda a ganinsa zai taimaka a samu daidaituwar darajar takardun kuɗin. Kazalika wata muhimmiyar shawarar da ya bayar a cikin jawabin nasa shi ne game da batun gabatar da wani tsarin haraji bai ɗaya tsakanin ƙasashen Turai akan hada-hadar kuɗi. Irin wannan haraji zai zama tamkar adalci ne a kasuwannin hannayyen jari. Masu biyan haraji su ne suka ɗauki nauyin Euro miliyan dubu har sau dubu huɗu da rara na tallafi tun bayan ɓarkewar rikicin takardun kudin da ake fama da shi. A saboda haka a yanzu lokaci yayi da za a rama musu. Kusan dukkan wakilan majalisar Turan dai sun tafa wa Jose Manuel Barroso dangane da kiransa na ƙara ƙarfafa haɗin kan Turai. An ma dai saurara daga bakin Martin Schulz, kakakin 'yan Socialdemokrats yana mai bayanin cewar:

"Mun daɗe muna sauraron irin wannan jawabi da kakkausan harshe domin kare makomar haɗin kan Turai ko ta halin ƙaƙa."

Europäisches Parlament in Straßbourg
Majalisar Turai a StraßbourgHoto: EU

A dai halin da ake ciki yanzu majalisar Turan ta albarkaci wata dakardar doka dangane da daidaita darajar takardun kuɗin Euro. A ƙarƙashin dokar za a ɗauki tsauraran matakai fiye da yadda lamarin yake a zamanin baya dangane da ƙasar da ta zarce abin da aka ƙayyade na basusukan gwamnati da giɓin kasafin kuɗin ƙasa. Za a ci tarar abin da ya kai kashi sufuli da ɗigo biyu cikin ɗari na jummular abin da ƙasa ke samarwa a shekara muddin ta kasa shawo kan matsalar gibin kasafin kuɗin a cikin watanni ƙalilan.

Mawallafi: Martin Bohne/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman