Matsalar makamai masu guba a Siriya
September 10, 2013Kantomar kula da manufofin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Catherin Ashton, ta bayyana yin marhabin lale da shawarar da kasar Rasha ta bayar, dangane da baiwa Majalisar Dinkin Duniya hurumin kulawa da makamai masu gubar da Siriya ta mallaka, domin lalatasu daga baya. Ashton, ta ambata cikin wata sanarwar da ta fitar cewar, tana goyon bayan wannan mataki, wanda ta ce kamata yayi sassan da abin ya shafa su yi aiki tukuru kuma cikin hanzari domin tsara daukacin bayanan da suka shafi hakan.
Dama ministan kula da harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya ce Rasha na yin aiki kafada-da- kafada da gwamnatin Siriya, domin tsara matakan aiwatar da shawarar da ta shafi makamai masu gubar, wanda kuma za su gabatar nan bada dadewa ba. Bayan hakane kuma, a cewar Lavrov zai kammala shirin, tare da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon da kuma Kungiyar Haramta Amfani da Makamai Masu Guba.
A martanin da ta mayar, Ashton, ta ce Kungiyar Tarayyar Turai mai kasashe wakilai 28, na goyon bayan wannan shawarar, da kuma aiwatar da ita yadda ya dace.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal