1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Ghana tana fuskantar matsalar hada wuta ta barauniyar hanya

April 19, 2022

A kasar Ghana amfani da wutar lantarki ta hanyar hada wutar ta barauniyar hanya ta gawurta musamman a yankin arewacin kasar, inda ake rasa makuden kudin shiga saboda hada layukan wutar lantarkin ta barauniyar hanyar.

https://p.dw.com/p/4A70d
Afirka na'aurar gwada wutar lantarki
Afirka na'aurar gwada wutar lantarkiHoto: DW

A kasar Ghana amfani da wutar lantarki ta hanyar hada wutar ta barauniyar hanya ta gawurta musamman a yankin arewacin kasar, inda kamfanin samar da wutar lantarki ke rasa makuden kudin shiga saboda hada layukan wutar lantarkin ta barauniyar hanyar. Sai dai kamfanonin sun fito da tsarin samar da mitar wuta ta zamani abin da ya janyo takun-saka tsakanin mutane da kamfanin.

A watan Janairu ma'aikatan kamfanin samar da wutar lantarki na arewacin Ghana suka isa gidan Abdallah Harun a garin Tamale domin sauya masa mitar tantance sanin wutar lantarkin da ya yi amfani da ita, da na zamani, amma ya nuna tirjiya kan matakin.

Kasuwa a birnin Accra | Ghana
Hada-hada a kasuwar Kaneshi da ke birnin Accra na kasar GhanaHoto: Christian Thompson/Anadolu Agency/picture alliance

Baya ga tunanin da wasu mutane da suke da shi na hada baki domin a cuci mutane da sabuwar mitar, akwai kuma wata gagarumar matsala da satar wutar da ke zama mai sauki da tsohuwar mitar. Mariam Yakubu ta hada layin wutar ta barauniyar hanya aka kama ta. Kamfanin ta maye gurbin mitar da take amfani da ita da ta zamani, sai dai Mariam Yakubu ba ta ji dadin haka ba, domin yanzu tana biyan kudin Ghana na Cedi fiye da yadda take biya a baya.

A kasashen Afirka da dama ana samun matsaloli wajen samar da mai wanda galibi ake amfani da shi kan samar da wutar lantarki, da hada wutar lantarki ta hanyar da ta saba ka'ida. A kasar Yuganda ga misali an yi asarar dubban miliyoyi na dalar Amirka saboda irin wannan al'ada. Shi ma kamfanin samar da hasken wutar lantarki na Ghana kashi 45 cikin 100 na wutar da yake samarwa na tafiya ta hanyar masu hada wutar lantarki ta barauniyar hanya.

A kasashe da dama na Afirka an saka irin wannan sabuwar mita kamar kasashen Kenya, da Zimbabuwe da Malawi da Yuganda. Sai dai yanzu a Ghana galibin mutane sun nuna adawa da matakin.