1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar cin hanci da rashawa a Girka

March 4, 2013

Kotu ta yankewa tsohon ministan tsaron Girka hukuncin daurin shekaru takwas bisa laifin cin hanci.

https://p.dw.com/p/17pyE
Former Greek defence minister Akis Tsochadzopoulos, addresses the Greek Parliament, in Athens, on Thursday, April 28, 2011. Lawmakers were voting Thursday on a proposal by the governing Socialist majority for a preliminary parliamentary investigation into whether Tsochadzopoulos was involved in possible bribery and money laundering in connection with a 2000 submarine contract. The deal was for the construction of three submarines for the Greek Navy by a consortium made of Greece's Hellenic Shipyards S.A. and Germany's Ferostaal and HDW. (ddp images/AP Photo/ Petros Giannakouris)
Akis TsohatzopoulosHoto: AP

Kotu ta yankewa tsohon ministan kula da harkokin tsaro a kasar Girka Akis Tsochadzopoulos, hukuncin daurin shekaru 8 a gidan yari, bayan da ta same shi da laifin mika takardun karya a lokacin bayyana irin kudaden shigar daya ke samu, a wani bangare na shari'ar cin hancin da take daukar hankali a cikin kasar ta Girka wadda ke fama da rikicin kudi. Hakanan kuma, kotun ta umarci tsohon ministan, wanda ke zama jigo a jam'iyyar Socialists, wadda ke zama tsohuwar jam'iyyar da ke tafiyar da mulki a kasar, daya biya tarar kudi ta Euro dubu 520, kwatankwacin dalar Amirka dubu 676, kana da bayar da umarnin kwace wani gidansa da ke tsakiyar Athens, babban birnin kasar ta Girka. Sai dai kuma tsohon ministan ya yi watsi da zargin cewar ya yi karya wajen bayyana kudaden shigarsa ne domin gujewa bayyana kudaden daya samu a tsakanin shekara ta 2006 da kuma 2009. Ko da shike yana da 'yancin daukaka kara akan shar'ar amma gabannin sake sauraren karar, zai ci gaba da kasancewa a gidan yari.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar