Matsalar baƙin haure masu zuwa Turai
January 2, 2014Talla
Rundunar sojan ruwan ƙasar Italiya suna kan ceto mutane 233, da ke cikin wani kwale-kwale, a kan hanyarsu ta shiga Italiya bisa ɓarauniyar hanya. Rahotanni suka ce wani jirgin helikoptan ƙasar Italiya ne ya haggo kwale-kwalen a cikin daren jiya. Akasarin baƙin haure da ke ciki, 'yan asalin ƙasashen Najeriya, Eriteriya, Somaliya, Pakistan, Zambuiya da Mali ne. Ganin yawan mutane da ke maƙare cikin kwale-kwale, ya sa sojan ruwan Italiya ƙaddamar da aikin na dokar ta-ɓaci don kawo ceto cikin gaggawa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu