1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko kun san ana auren wuri a Amirka?

September 8, 2020

Kididdiga na nuni da cewar tsakanin shekarun 2000 zuwa 2010, yara mata masu karancin shekaru dubu 248 ne suka yi aure a Amirka, mafi yawansu kuma na dole.

https://p.dw.com/p/3iAat
Kinderehe in Afrika
Miliyoyin yara kanana ake wa auren wuri a wasu kasashen duniya, ciki har da AmirkaHoto: picture-alliance/obs/Peter Rigaud

Genevieve Meyer ba za ta taba mancewa da yadda ta auri mijinta mai shekaru 42 a duniya a lokacin da take 'yar shekaru 15 da haihuwa kacal ba. Ita da mahaifiyarta na rayuwa a wani mawuyacin yanayi a wurin ajiyar manyan motocin dakon kaya. Sai mutumin ya yi alkawrin cire ta daga wannan kangin rayuwa. Sai suka yi aure, bayan amincewar mahaifiyartata a rubuce. Hakan ya halalta aurenshi da Genevieve Meyer kamar yadda ta bayyana: "Na lura da cewar a kullum yana kallona idan ina wucewa, kwatsam rana guda sai ya ce: "barka dai, hala ke bakuwa ce a nan?""

Karin Bayani: UNICEF: Milyoyin yara mata kan fuskanci auren wuri

Yawancin auren da ake wa yara mata tun suna da kananan shekaru dai na tilas ne ba tare da amincewarsu ba. Fraidy Reiss ita ma, daya ce daga cikin irin 'yan matan da suka tsinci kansu cikin wannan yanayi. Iyayenta wadanda Yahudawa ne, su suka zabarwa 'yar shekaru 19 da haihuwar mijin da ta aura a wancan lokacin. Auren da ya hanata 'yancin ci gaba da karatu ko samun horo kan makamar aiki, ballantana mallakar asusun banki na kanta.

Matsalolin auren wuri a Najeriya

Ya dauki Fraidy Reiss shekaru 12 kafin ta samu nasarar ballewa daga wannan auren na dole. Sai dai iyayenta da ke zama masu addini ne sosai, sun yanke duk wata hulda da ita har kawo yanzu. Reiss ta bayyana cewa:  "Mutane na mamakin ganin ana fuskantar wadannan matsalolin a Amirka."

Ta kafa wata kungiya mai suna " Daga karshe na samu 'yanci." Mai 'ya'ya biyu a yanzu haka, Reiss ta dukufa ka'in da na'in wajen ceto 'yan mata kanan daga auren dole a Amirka. A hukumance dai ba a amince da auren yara kanana ba, sai dai idan iyaye sun amince ko kuma ta samu juna biyu ko alkali ya amince. A yankunan karkara ko kuma a tsakanin talakawan Amirka alal misali, ana yawan samun matsalar aurar da kananan yara saboda dalilai na al'adu ko kuma addini.
A cewar Fraidy dai, mafi kankancin irin wannan auren shi ne, 'yar shekaru 12 da haihuwa: "Wajibi ne mu tabbabatar da cewar, sai yaran sun kai shekarun balaga kafin su rattaba hannu a irin wannan takardar doka ta aure. Ta haka ne zasu samu 'yanci kamar na manya, na barin auren. Kana a basu gidan da aka tanada domin irin wadannan matan, su samu lauya kasancewar wadannan abubuwa ne da suke da wahalar samu a bangaren yara kanana".

Protestaktion in Berlin Terre des Femmes Frauenrechtsorganisation Kinderehe
Zanga-zangar adawa da auren wuri a Berlin fadar gwamnatin JamusHoto: Imago

Karin Bayani: Yaki da al'adar auren wuri a Afirka

Akwai dai sarkakikya a wannan lamari: Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta bayyana aurar da yara kanana a matsayin take hakkin dan Adam ne. Sai dai a daya hannun, jihohin kasar guda hudu ne kadai suka haramta aurar da kanan yara. Jihohin kuwa su ne Delware da New Jersey da Pennsylvania da Minnesota. Kuma a 'yan shekarun da suka gabatta ne kawai, dokar ta fara aiki a jihohin.

Karin Bayani: Nijar na bukatar dokar hana auren wuri

Akwai dai illoli da ke tattare da aurar da yara tun suna kanana. Akasarinsu basa samun damar kammala karatunsu, a yawancin lokuta suna rayuwa cikin talauci, inda mazajen nasu ke cin zarafinsu ta hanyar duka. Daura da komai ma, auren yara kanana ba ya dorewa, saboda irin cin zarafi da mugunta da ke cikinsa.